Yin wa’azi ya yin rufe mamaci

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin wa’azi ya yin rufe mamaci

Tambaya

Shin ya halasta ayi wa mahalta jana’iza wa’azi ya yin rufe mamaci?

Amsa

Babu laifi ayi wa’azi takaitacce domin tunatar da mutane lahira a ya yin rufe mamaci, an karbo daga Amirul-muminina Aliyu Allah ya girmama fuskarsa inda ya ce: (Mun kasance tare a wurin wata jana’iza a makabartan Bakiyal Garkad, sai Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya zo mana, sai ya zauna, muma sai muka zauna a gefensa, a tare da shi akwai wata sanda a hannunsa yana caka sandar a kasa sannan sai ya ce: “Babu wani daga cikinku babu wata rai mai nunfashi face sai an rubuta mata makomarta na daga Aljanna ko kuma wuta, idan ba haka ba kuma an riga an rubuta mata matsayinta na kasancewa ‘yar wuta ce ko ‘yar Aljanna” sai wani mutum ya ce:Ya Manzon Allah, shin ba ma dogara ga abin da aka riga aka rubuta mana ba? Sai Manzon Allah ya ce: “Kuyi aiki, kowani ma’abocin aiki an saukake masa yin aikinsa”) An yi ittifaki akansa.

Share this:

Related Fatwas