Ta’assubanci da tsaurin ra’ayin addini
Tambaya
Mene ne tasirin da ta’assubanci da tsaurin ra’ayin addini suke yi wa al’umma?
Amsa
Dukan nau’o’in ta’assubanci da tsaurin ra’ayi na addini, abubuwa ne da suke rusa al’amurran addini da na rayuwa gaba daya, kuma dukansu suna cutar da zaman lafiyar rayuwar al’umma, suna kuma yada kiyayya da keta da fitina a cikin kasa, lallai an riga an sifanta wannan al’umma da ma shari’arta da cewa matsakaita ne, kaman yanda Allah Madaukaki ya ce: (Kaman haka muka sanya kuka zama al’umma matsakaiciya; saboda ku zama shaidu ga sauran mutane, ku kuma Manzon Allah ya zama shaida a gare ku) [al- Bakra: 143], an kuma sanya tsaurin ra’ayi da ta’assubanci suka zama nau’o’i ne na fita daga mutuntaka, da komawa da ita baya zuwa ga kwazazzaban son zuciya da sha’awa na kaskanci.