Sauraron mamata ga wadanda suka ziyarcesu ko sukayi musu sallama da kuma jin cewa an ziyarce su?
Tambaya
Shin mamata suna jin wadanda suka ziyarce su a kaburburansu?
Amsa
Yana daga cikin abin da aka sani cewa shi mutum idan ya mutu, to mutuwarsa baya nuna karewarsa na gaba daya ko kuma rashinsa na har abada wanda ransa ba zai sake komowa ga jikinsa ba, amma gaskiyan lamari shi ne wani mataki ne na ciruwa daga wata rayuwa zuwa wata rayuwar ta daban, don haka a wannan yanayin mutum zai iya riskan duk abin da ke kusa da shi, yana iya jin wanda ya ziyarce shi, yana mayar da sallamar da aka yi masa, wannan yana daga cikin abubuwan da suka tabbata daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam a cikin hadisai masu yawa: kamar dai Hadisin bijirar da ayyuka ga Mustapha SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam da nema mana gafara da yake yi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam inda ya ce: (Rayuwata alheri ne gareku, kuna aikata abubuwa sannan hukuncinsu na zuwa a lokacin, sannan mutuwana alheri ne gareku, ana bijiro mini da ayyukanku, duk abin da nagani na alheri sai na godewa Allah, duk abin da na gana na sharri sai na nema muku gafara), Bazzar, malamai da yawa sun inganta wannan Hadisin daga cikin kwararrun malaman Hadisi, kamar Imam Nawawi da Al’Hafeez Ibn Hajr, da Alhafeez Suyudi da wasunsu.
Haka nan yana daga cikin abin da ya zo cikin shari’a na shar’anta lakkanawa mamaci kalmomi, da a ce shi mamaci baya amfanuwa da lakkanawan, to da ba a shar’anta hakan ba.