Adadin raka’o’in nafila da lokacins...

Egypt's Dar Al-Ifta

Adadin raka’o’in nafila da lokacinsu

Tambaya

Nawa ne adadin raka’o’in nafila da lokutansu?

Amsa

Sallolin da ake gabatarwa kafin sallolin wajibai, ko bayansu, ko dai su zama sunna ne mai karfi, watau wadda Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya rinka yi ba tare da yankewa ba, wanda suka zo a cikin Hadisi mai daraja: (Wanda ya dage akan raka’o’i goma sha biyu a dare da rana, ya shiga aljanna, raka’a hudu kafin Azuhur, raka’a biyu bayanta, da raka’a biyu bayan Magriba, da raka’a biyu bayan Isha’i, da raka’a biyu kafin fitowar alfijir) [an- Nasa’i].

Ko kuma su zama sunna ba mai karfi ba, an so a gabatar da su, ba tare da an tabbatar ba, wadanda su ne raka’a biyu kafin La’asar, da raka’a biyu kafin Magriba, da raka’a biyu bayan Isha’i, saboda Hadisin da jama’a masu yawa suka ruwaito daga Abdullahi Bn Mugaffal (Allah ya kara yarda da shi), cewa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Tsakanin dukan kiran sallah biyu akwai sallah, tsakanin dukan kiran sallah biyu akwai sallah –sannan a na uku ya ce- ga wanda yake so); gudun kada mutane su dauki hakan a matsayin sunna. Ire- iren wadannan sunnoni su ake kira da sallar nafila ko tadawwu’i.

Share this:

Related Fatwas