Damfara ko 419

Egypt's Dar Al-Ifta

Damfara ko 419

Tambaya

Mene ne hukuncin shari’a game da damfara da 419?

 

Amsa

Abin da ‘yan damfara da 419 suke yi haramun ne a shari’ar Musulunci, dokokin kasa kuma sun sanya haka a matsayin laifi, saboda harka ce da aka ginata akan yin amfani da rashin sanin talakawa, a wasu lokuta akan boya ta mayafin shari’a, ba a yin la’akari da ka’idojin da shari’a ta shinfida a cikin mu’amala, domin ta ginu ne akan algushi, da rufa- rufa, da ha’inci da cin amana, da cin dukiyoyin mutane ta hanyar barna; domin wanda yake damfara ko 419 da wanda ake damfara dukansu suna neman su sami kudi ne ta haramtacciyar hanya, da kuma rashin samun lamuni na doka ga masu kudaden, sannan kowa ya san da cewa akwai rudi da jahilci da lalata dukiyoyin da Allah Madaukakin Sarki ya bayar da umurnin a kiyaye su. Sannan kuma masana tattalin arziki sun bayyana cewa irin wannan mu’amalar tana matukar cutar da tattalin arzikin kasa, ta kuma ci karo da manufofin shari’a, domin bai wa kasashe kariya a bangaren tattalin arziki manufa ce babba daga cikin manufofin shari’a, duk wanda yake kawo masu cikas to ya yi laifi.

Share this:

Related Fatwas