Ayyukan kisan gilla

Egypt's Dar Al-Ifta

Ayyukan kisan gilla

Tambaya

Shin ya halasta yin ayyukan kisan gilla kamar dai yanda masu tsattsauran ra’ayi ke yi?

Amsa

Bai halasta arinka yin irin wadannan munanan ayyukan ba, saboda hakan ya ci karo da manufofin shari’a mai girma da ke mayar da hankali wurin kiyaye rai wacce Allah ya haramta yi mata ta’addanci ba tare da wani hakki na shari’ba, kamar kisasi ko yakar mai ta’addanci, to fa duk wanda yake aikata irin wannan danyen aikin hukuncinsa a musulunci shi ne hukuncin wanda ya yi kisa na ganganci, saboda da gangan ya kasha ran ba tare da wani dalili ba, wanda kuma akwai shiri da niyya akan haka, Allah Ta’ala yana cewa : (Duk wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakonsa shi ne dawwama cikin wutar Jahannama, sannan Allah ya yi fushi da shi, ya kuma la’ance shi, kuma ya yi masa tanajin azaba mai girma) {Nisa’a 93} Babu banbanci tsakanin yiwa musulmi kisan gilla da wanda ba musulmi ba, hakika Annabi SallaHu AlaiHi wasallam yaki amsar uzurin Harith bin Suwaid wanda ya yiwa Al’Mujzir bin Ziyad kisan gilla.

Kamar yanda yake bayyana shi kisan gilla na haifar da barna da wufintar da jini, tare da gurgunta harkar tsaro da zaman lafiya, don haka kisan gillake yana cikin layin ayyukan yaki da aka hana a musulunci.

A jumlance dai duk ayyukan kisan gillan da masu tsattsauran ra’ayi ke aikatawa ya sabawa koyarwar addini domin ya haramta shi, hakanan dokar kasa ta yi tanaji mai tsanani ga duk wanda ya aikata hakan.

Share this:

Related Fatwas