Kiyaye tsafta a wurare mallakar al’umma
Tambaya
Yaya addinin Musulunci ya kwadaitar da mu wajen kiyaye tsafta a wurare mallakar al’umma?
Amsa
Ita tsafta –ta al’umma da ta jiki- abu ne da shari’a ta nemi a yi; wajibi ne mutum ya kula da ita a cikin dukan al’amurransa, saboda tsafta daya ne daga cikin muhimman hanyoyi na kiyaye lafiya, wadda take babban ni’ima ce da Allah Madaukakin Sarki ya yi wa dan Adam, saboda haka ne malamai suka bayyana cewa mustahabbi ne kiyaye tsaftar gidaje da wurin zama, wurare mallakar al’umma ma ya shiga cikin wannan; kai ma kiyaye tsaftar wurare mallakar al’umma ya fi zama kan gaba; ganin cewa rikon sakainar kashi da tsaftar su zai iya haifar da cutar da lafiyar al’umma.