Karya doka wajen sayar da magungunan inshora
Tambaya
Wasu masu sayar da magunguna suna sayen magungunan inshora su sayar wa mutanen da ba su aka samar da magungunan dominsu ba a dakunan sayar da magunguna na kashin- kansu, mene ne hukuncin wannan?
Amsa
Magungunan inshore ba hakkoki ne da ake mallaka a karan kansu ba, a’a magunguna ne da ake bai wa marasa lafiya daidai da tsarin shan maganin da ya dace da su gwargwadon lokacin da aka ba su na shansu a lokutansu, gwamnati ne take daukan nauyin sayensu, take kuma sanya wa masu bukatansu sharadin cewa ba za su sayar ba; saboda haka suna cikin dukiyoyin al’umma, suna cikin “bayar da dama” ne ba “mallaka” ba, saboda haka haramun ne a yi hada- hadar saye da sayarwa da su, bugu da kari, ga kuma irin cutarwar da haka yake yi wa bangaren lafiya, da kuma yada cin- hanci da rashawa, da zaluntar hakkokin marasa lafiya.
Aikata haka, ko taimakawa a aikata haka da wasu daga cikin masu dakunan sayar da magunguna ko wasunsu –da aka amince masu wajen isar da wannan maganin zuwa ga masu bukatansa- suke yi ha’inci ne da cin- amana; wanda ya aikata wannan ya cancanci a yi masa ukuba da azaba a ranar alkiyama; a duniya kuma a hukunta shi daidai da yanda doka ta tanada.