Domin Annabi (SallalLahu alaiHi wa ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Domin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da Ahlul baiti, ko domin Ka’aba

Tambaya

Mene ne hukuncin mutum ya yi wa waninsa magiya saboda ya biya masa bukatarsa, ta hanyar cewa: domin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da Ahlul baiti, ko domin Ka’aba?

Amsa

Kamun kafa, ko tabbatar da zance da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ko da waninsa, kaman mutum ya ce: don Annabi, ko na rantse da Ka’aba da sauransu, da ba manufarsu yin rantsuwa ta hakika ba, abu ne da ya halatta a shari’a, babu wata matsala a wurin jamhur din malamai masana fikihu, bai kuma kamata a hana yin haka dogaro da dalilai na zahiri da suke haramta yin rantsuwa da wanin Allah ba; ba ma a babi daya suke ba, irin haka ya zo a cikin maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da maganganun manyan sahabbai; an ruwaito Hadisi daga Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: wani mutum ya zo wurin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sai ya ce: ya Manzon Allah, wace sadaka ce ta fi girman lada? Sai (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ai kuwa na rantse da babanka, za a fada maka, shi ne ka yi sadaka kana cikin koshin lafiya, kuma kana son abin da z aka yi sadaka da shi din, kana tsoron talauci, kana kuma fatan dawwama) har zuwa karshen Hadisi.

Bukhari da Muslim sun ruwaito cewa matar sayyiduna Abubakar al- Siddik (Allah ya kara yarda da su) ta ce masa: “Ai kuwa na rantse da sanyin idanuwana; lallai yanzu ya rubanya haka har sau uku akan yanda yake a baya” tana nufin abincin bakinsa.

Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas