Misanya sabon zinare da tsoho
Tambaya
Shin ya halasta a misanya sabon zinare da tsoho?
Amsa
Babu laifi a shari’ance a misanya tsohon zinare ko kuma wanda ya karye da sabon zinare, ko kuma irin wanda aka sabunta tare da kiyaye bayar da cikon kudin da yake na banbanci tsakanin sabon da tsohon, ba tare da sharadin amsar kudin tsohon ba a karon farko, sannan sai a biya kudin sabon zinare bayan haka, ta inda za a daukewa misayan biyan kudi kafin ayi, domin a samu dalilin samuwar sana’a da abinda aka kera kamar dai kowani kayan ciniki wanda ba a haramta tafaduli a cikinsa ba, ko kuma sayar da abinda yake mai jinkiri.